<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>44</hymn_number>
<title>Littafi Mai Tsarki, Abincin Rai Ne Shi Y44</title>
<lyrics>[V1]
 'Y44
 1)Littafi Mai Tsarki, abincin rai ne shi,
 Akwai ƙoshi, sai ka za ka ci
 Littafi Mai Tsarki

[V2]
 2)Littafi Mai Tsarki, saƙon Ubangiji,
 A cikinsa, aka bayyana
 Ҡauna ga Masu Bi

[V3]
 3)Littafi Mai Tsarki, fitilar Masu Bi,
 Haske 'na nan, za ya kai mu can,
 Littafi Mai Tsarki.

[V4]
 4)Littafi Mai Tsarki, ya zama takobi
 In ya shiga cikin zuciya,
 Zai tone zunubi.

[V5]
 5)Littafi Mai Tsarki, cike de ilimi,
 Bincikensa dai da gaskiya
 Zai ba ka fahimi.

[V6]
 6)Littafi Mai Tsarki, jawabin Masu Bi,
 Maganarsa mu ke shelarta,
 Littafi Mai Tsarki.

[V7]
 7)Littafi Mai Tsarki, iri mai kyau ne shi,
 Da aminci za mu shuka shi
 A duniyan nan yanzu.

[V8]
 8)Littafi Mai Tsarki, shi kaɗai mu ke bi
 Amfaninsa da daɗinsa
 Sun wuce misali.</lyrics>
</song>